Hatsarin tirela ya yi ajalin mutum 25 a Neja

0
158

Wata tirela da ke ɗauke da kusan mutum 230 a cikinta ta yi hatsari a Jihar Neja, inda aƙalla mutum 25 suka rasu nan take.

Bayanai sun nuna motar ta yi hatsarin ne ita kaɗai a ƙauyen Takalafiya da ke kan babbar hanyar Yawuri a ƙaramar Hukumar Magama ta Jihar Neja.

A cewar Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan Jihar, Bologi Ibrahim, Gwamnan Jihar, Mohammed Umar Bago, ya damu matuka da hatsarin sannan ya buƙaci direbobi su daina karya dokokin tuƙi.

Ya ce hatsarin, wanda aka yi ranar Talata ya faru ne sakamakon gudun wuce sa’a, wanda ya sa motar ta ƙwace daga hannun direbanta.

Bayanai sun nuna tirelar dai ta taso ne daga Jihar Sakkwato ɗauke da mutum 229, waɗanda suka haɗa da maza da mata da ƙananan yara a cikinta.

KU KUMA KARANTA: Mutum 4 sun mutu a Abiya, wasu sun jikkata a hatsarin mota

Rahotanni sun ce nan take mutum 25 suka mutu, yayin da wasu da dama suka samu munanan raunuka kuma yanzu aka garzaya da su Babban Asibitin Kontagora, inda suke samun kulawa.

Kazalika, waɗanda suka rasu yanzu haka an kai gawarwakinsu ɗakin adana gawarwaki na asibitin na Kontagora.

Leave a Reply