Manoma sun koka kan yadda makiyaya ke cinye musu gonaki a Gombe

0
155

Wasu manoma a yankin garin Chilo da ke ƙaramar hukumar Akko ta Jihar Gombe, sun koka kan yadda makiyaya ke kaɗa dabbobinsu cikin dare suna cinye musu gonaki.

Manoman sun ce sun kama shanun makiyayan inda suka miƙa wa kwamitin da gwamnati ta kafa kan hana makiyaya shiga gonakin al’umma.

Manoman sun ce da haɗin kan ‘yan banga suka samu nasarar kama makiyayan tare da shanunsu suka miƙa su ga kwamitin a Karamar Hukumar Yamaltu Deba.

Sai dai manoman sun ce suna zargin wasu daga cikin ‘yan kwamitin da sakin shanun, lamarin da ya sanya suke buƙatar gwamnati ta kawo musu ɗauki.

Wani manomi mai suna Malam Bello, ya bayyana wa Aminiya cewa cikin dare makiyayan suka bi suka cinye musu gonaki da suka shafe tsawon watanni huɗu suna nomawa.

KU KUMA KARANTA: An jikkata mutane da dama a rikicin makiyaya da manoma a Kano

Shi ma Dahiru Inusa, cewa ya yi suna neman alfarmar gwamnati da masu ruwa da tsaki su bi musu kadin amfanin gonakinsu da makiyayan suka lakwume dare ɗaya.

“Bayan mun kama shanun mun miƙa wa ’yan kwamiti sai su kuma suka saki shanun.

“Mun samu labarin cewa kwamitin da gwamnatin ta kafa sun mayarwa da Fulanin shanunsu ne bayan miƙa musu da suka yi don ɗaukar mataki.

“Hakan zai iya bai wa Fulanin damar sake dawowa su cinye sauran abin da ya rage a gonakin.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin ’yan kwamitin ko Shugaban ƙaramar hukumar Yamaltu Deba, amma lamarin ya ci tura.

Sai dai wata majiya a ƙaramar hukumar da ta buƙaci a sakaya sunanta, ta shaida cewa ’yan kwamitin sun mayar wa makiyayan shanun ne saboda nauyin ɗawainiyar ciyar da su.

Leave a Reply