Sojoji sun fatattaki ’yan ta’addan hanyar Kaduna zuwa Abuja

0
210

Rundunar Sojin Sama ta ‘Operation Whirl Punch’ ta fatattaki ’yan ta’adda da dama a wani ɓarin wuta da ta yi a ƙaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Daraktan yaɗa labarai na rundunar sojin saman Najeriya, Air Commodore Edward Gabkwet ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

Ya ce an fara aikin ne bisa bayanan sirri da ke nuna akwai wani kasurgumin ɗan ta’adda da aka fi sani da Boderi tare da ɗan uwansa Nasiru da sauransu a maɓoyarsu da ke ƙauyen Tsaunin Doka a yankin.

“Jirgin sojojin saman Najeriya ƙarƙashin Operation Whirl Punch sun ci gaba da kai hare-hare ta sama kan ‘yan ta’addar da ke shiyyar Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, wanda ya kai ga halaka wasu ‘yan ta’adda a Tsaunin Doka da ke ƙaramar hukumar Igabi ta Jihar Kaduna.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Daga baya, an kai hare-hare ta sama a wurin da sanyin safiyar ranar 16 ga watan Nuwamba, 2023, inda aka yi nasarar fatattakar da yawa daga cikinsu.

KU KUMA KARANTA: Sojoji sun kama masu ƙera haramtattun makamai a Filato

“An kuma kai harin wannan hari a maboyar ‘yan bindigar tare fatattakar Boderi. Dukkanin hare-haren biyu an yi nasara kuma an fatattaki ‘yan bindiga kuma an yi nasara.”

Air Commodore ya bayyana cewa Boderi da mukarrabansa suna da alhakin kai hare-hare da sace-sace da dama a hanyar Abuja zuwa Kaduna, hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari, da kuma wasu yankuna a jihohin Kaduna da Neja.

Leave a Reply