An saki dubban fursunoni don rage cunkoso a gidajen yari

0
129

An saki dubban fursunoni daga gidajen yari daban-daban a Najeriya a yunƙurin gwamnatin ƙasar na rage cunkoso a gidajen, kamar yadda Ministan Harkokin Cikin Gida na kasar Olubunmi Tunji-Ojo ya bayyana a shafinsa na sada zumunta a karshen mako.

Wannan yana cikin ƙudirin shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu, wanda aka zaɓe shi a farkon shekarar nan, na rage cunkoson gidajen kaso, a cewar ministan.

“Jiya sun soma sakin fursunoni 4,068 cikin 80,804 da ke gidajen gyaran hali 253 a faɗin ƙasar nan, waɗanda ake tsare da su saboda sun gaza biyan tarar da aka sanya musu,” in ji Olubunmi Tunji-Ojo a sakon da ya wallafa a shafinsa na X, wanda a baya ake ƙira Twitter.

Ya sanar da ɗaukar matakin ne bayan ya kai ziyara gidan yarin Kuje da ke Abuja babban birnin ƙasar.

Kakakin ministan Ajibola Afonja ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa “fursunonin da tarar da aka sanya musu ba ta wuce ta naira miliyan ɗaya ba ne kaɗai za su ci moriyar wannan shiri.”

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Iran ta yi afuwa ga fursunoni 1,000 albarkacin ranar Maulidi

Afonja ya ƙara da cewa sun soke tarar da ta kai naira miliyan 585 da aka sanya wa wasu fursunoni.

Tinubu ya yi alƙawarin ɗaukar sabbin matakai na rage yawan fursunoni a gidajen yari, yana mai cewa za a rika hukunta masu laifi ta wasu hanyoyin ba tare da an garkame su ba.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce adadin fursunonin da ke gidajen yarin Najeriya ya zarta kashi 147 na waɗanda ya kamata su kasance a ciki kuma mutanen da aka tsare kan kwashe shekaru ba tare da an kammala shari’arsu ba.

Leave a Reply