An baza ƙarin sojoji da ‘yan sanda a Kano gabanin hukuncin kotu kan shari’ar Abba da Gawuna

0
186

Rundunar ‘yan sandan Kano ta ce an jigbe ƙarin sojoji da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a faɗin jihar don wanzar da tsaro gabanin hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara za ta yanke a shari’ar gwamnan jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Mohammed Usaini Gumel ne ya bayyana haka a taron manema labarai da ya gabatar ranar Alhamis da maraice a birnin na Kano.

“Matsayar rundunar ‘yan sandan Kano da sojoji da sauran jami’an tsaron jihar ita ce, mun kammala haɗa gwiwa don ɗaukar dukkan matakan tsaro don tabbatar da zaman lafiya kafin hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara da lokacinsa da kuma bayansa.

“Za ku ga cewa mun ƙara jami’an tsaro na dukkan hukumomin tsaro a muhimman sassa domin tabbatar da ganin ba a fuskanci karya doka da oda ba a dukkan sassan jihar nan,” in ji Kwamishina Gumel.

Ya ƙara da cewa hukumomin tsaro sun tattauna da wakilan jam’iyyar APC da NNPP “kuma mun amince cewa hanya mafi a’ala ita ce ta tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali kafin hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara da lokacin yanke shi da kuma bayansa.”

KU KUMA KARANTA: An bayyana inda za a saurari shari’ar zaɓen gwamnan Kano da na sauran jihohi

Kwamishinan ‘yan sanda Gumel ya ce,” Mun samu tabbaci daga jam’iyyun biyu cewa za su isar da sako ga magoya bayansu. Muna masu tabbatar muku cewa shugabannin jam’iyyun sun sanya hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya a ofishin kwamishinan ‘yan sanda.”

Dangane da haka, rundunar ƴan sandan ta ba da shawarwari kamar haka:

i. Ba za a yarda da taron mutane a ko ina ba da kuma kowace irin manufa

ii. A guji shiga cikin manyan ayyuka da bayar da shawarar shirya zanga-zangar tashin hankali da yin zanga-zanga ko wasu tarukan murna da ka iya jawo martani daga wani ɓangaren.

iii. Ƴan siyasa su guji yin kalamai barkatai waɗanda ka iya haifar da tashin ko kuma ɓata shirye-shiryen samar da tsaro da taɓa fannin shari’a.

Leave a Reply