Isra’ila ta ƙi amincewa da ƙudirin MƊD na tsagaita wuta

Ma’aikatar Harkokin Wajen Isra’ila ta yi watsi da ƙudirin da Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya wanda ya amince a “tsagaita wuta” a Gaza.

A wata sanarwa da jaridar Haaretz ta wallafa, ta ambato ma’aikatar tana cewa “babu wata kafa ta tsagaita buɗe wuta” muddin ƙungiyar Hamas ta Falasɗinawa ta ci gaba da rike mutanen da ta yi garkuwa da su.

Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ranar Laraba ya amince da wani daftari wanda ya yi ƙira a “gaggauta tsagaita wuta” a faɗin Gaza.

Kasashe goma sha biyu ne suka amince da ƙudurin wanda ƙasar Malta ta gabatar, yayin da Amurka da Birtaniya da Rasha suka ƙaurace wa kaɗa ƙuri’a.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *