Ba don kishin ƙasa ‘yan ƙwadago suka tsunduma yajin aiki ba – Gwamnati

0
193

Daga Haruna Idi Hassan

Gwamnatin tarayya ta bayyana taƙaicinta ƙan matakin da ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya ta yanke na ƙiran ma’aikata da su tsunduma yajin aiki daga tsakar daren 13 ga watan Nuwamba duk da umarnin hana ƙungiyar tsunduma yajin aiki a makon jiya da Mai Shari’a Benedict Backwash Kanyip na Kotun Masana’antu ta ƙasa ya bayar.

Wannan shawarar da NLC da TUC suka yanke, yunƙuri ne na yiwa gwamnatin zagon ƙasa kuma wannan sam ba abun lamunta ba ne.

Hakan na ƙunshe ne acikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman ƙan harkokin yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga ya fitar yayin da yake mayar da martani ƙan fara yajin aikin da ƙungiyar ta soma.

Har yanzu mun rasa dalilin da ya sa NLC da TUC suka yanke shawarar hukunta dauƙacin ƙasar nan mai mutane sama da miliyan 200 kan wani lamari na ƙashin kai da ya shafi shugaban NLC, Mista Joe Ajaero, wanda kuskuren hukuncin da ya yanke ne ya janyo masa hakan a Owerri a yayin da ya ke shirin tunzura ma’aikata a jihar Imo tsunduma yajin aikin da bai kamata ba.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta dakatar da ƙugiyoyin ƙwadago tafiya yajin aiki da suka shirya

“Yayin da gwamnatin tarayya ba ta lamunci duk wani nau’i na tashin hankali da cin zarafi ga kowane ɗan Nijeriya ba, duba da tsare mutuncin zamantakewa da harkokin tattalin arzikin ƙasa nan ta ke Sufeto Janar na ƴan sanda ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan abin da ya faru da Mista Ajaero yayin da Kwamishinan ƴan sanda na jihar Imo wanda lamarin ya faru a karkashinsa aka sauya masa wurin aiki zuwa wajen jihar.

Leave a Reply