Saudiyya ta soke bizar ’yan Najeriya 264 bayan saukarsu a Jidda

0
170

Gwamnatin Saudiyya ta soke bizar ’yan Najeriya 264 da suka je Umrah a daidai lokacin da Shugaba Bola Tinubu ke ziyarar aiki a ƙasar.

Saudiyya ta soke bizar ɗaukacin ’yan Najeriya 264 da suka je ƙasar daga Kano da Legas ne, ta kuma ba da umarnin a dawo da su gida ne a ranar Lahadi.

Saukar jirgin kamfanin Air Peace da fasinjojin ke da wuya a Jiddah, jami’an filin jirgin sama na Sarki Abdulaziz suka samu sanarwar cewa an soke bizar ɗaukacin fasinjojin da suka iso daga Najeriya.

Kafin barin Najeriya sai da aka yi wa fasinjojin tantacewa da binciken kwakwaf a filayen jirgi, da sanya idon hukumomin Saudiyya kuma aka tabbatar cewa bizarsu ba ta da matsala.

KU KUMA KARANTA: Za mu taimaka wa Najeriya ta gyara matatun manta – Saudiyya

Hakan ta faru ne a yayin da Shugaba Bola Tinubu da kusoshin gwamnatinsa suke halartar taron tattalin arzikin ƙasahen Larabawa da Afirka a Saudiyya, inda kuma suka yi Umrah.

Kimanin makonni biyu ke nan da Air Peace ya fara jigijalar fasinjoji kai-tsaye daga Najeriya zuwa Jidda.

“Muna zargin wannan wani shiri ne na sanya hakar fita a ran kamfanin, saboda akwai waɗanda ba su ji daɗin fara aikin Air Peace kai tsaye daga Najeriya zuwa Jidda ba, sabanin kamfanonin jiragen ƙasashen waje da suka fi shi tsada,” in ji wata majiya.

Aminiya ta gano daga bisani Ofishin Jakadancin Najeriya a Saudiyya ya rage adadin waɗanda za a dawo da su gida zuwa 177, waɗanda yawancinsu su tafi Saudiyya ne domin yin ibadar Umrah.

Kafin fara tashin Air Peace kai tsaye zuwa Jidda, kamfanin Saudiyya na yin wannan aiki.

Leave a Reply