’Yan ta’adda a Katsina sun kashe kwamandan jami’an tsaro

0
175

A ranar lahadi ne wata tawagar ’yan fashin daji ta kai wani mummunan hari a garin Zakka da ke ƙaramar hukumar Safana ta jihar Katsina.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, ’yan ta’addan sun kai harin ne da nufin ƙara nunawa tare da faɗaɗa munanan ayyukansu na ta’addanci.

Sai dai wannan hari ya gamu da cikas ta dalilin fitar jami’an tsaron da suka haɗa da sojojin sama da ’yan sanda tare da jami’an tsaron al’umma da ake ƙira da “Community Watch Corps”.

’Yan ta’addan sun gamu da tirjiyar jami’an tsaro da aka yi karon batta a tsakanin ɓangarorin biyu, wanda a dalilin haka kwamandan wannan jami’an tsaron na al’umma mai suna Mujitaba Salisu da wani ɗan sandan kwantar da tarzoma guda suka riga mu gidan gaskiya.

KU KUMA KARANTA: Sojojin Najeriya sun kashe ƴan bindiga bakwai a Kaduna

Kazalika, an yi wa ’yan daban dajin mummunar ɓarna, inda suka kwashe gawarwakin su suka koma daji kamar yadda suka saba.

Ana iya tuna cewa, a ’yan kwanakin nan wasu iyalai suka yi koken cewa waɗannan jami’an tsaron al’ummar sun kashe wani ɗan uwansu da wasu mutane biyu a garin na Zakka.

Ita dai ƙaramar hukumar Safana na ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin da ayyukan ’yan daban dajin suka yi ƙamari.

Leave a Reply