Uwa ta kashe ’yarta mai watanni 11 a Benuwe

0
136

Ana zargin wata matashiya da kashe ’yarta mai watanni 11 ta hanyar ba ta guba a ƙaramar hukumar Logo ta jihar Benuwe.

Matashiyar ta shiga hannu ne a ranar asabar a yayin da take ƙoƙarin jefar da gawar yarinyar, inda matasa suka damƙe ta suka miƙa ta ga ’yan sanda a unguwar Abeda-Mbadyul.

Jami’in yaɗa labaran ƙaramar hukumar Logo, Paul Pevikyaa, ya yi zargin maganin kashe ciyawa matashiyar ta ba wa ’yar tata ta kashe ta.

“Ta ce ta saurayinta ne ya yi mata cikin shege ta haifi ’yar, amma sai ya yi watsi da su, ita ke shan wahalar kula da ’yar, shi ya sa ta ba ta guba ta mutu,” in ji Pevikyaa.

KU KUMA KARANTA: An kama mutane huɗu da ake zargi da fashin banki a Benuwe, wanda ya yi sanadin mutuwar DPO da ‘yan sanda uku

Mai magana da yawun ’yan sandan Jihar Benuwe, SP Catherine ta tabbatar da faruwar lamarin kuma ta ce rundunar na gudanar da bincike.

Wani mazaunin yankin ya yi ƙira da a hukunta matar, wadda wasu jami’an lafiya suka yi zargin na fama da tsananin damuwa.

Wani mai faɗa a ji a yankin ya ce a cikin daren Juma’a ne ’yar ta kamu da rashin lafiya, cikin kimanin awa biyu ta ce ga garinku nan.

“Babu wanda ta sanar a cikin makwabta ba, kuma sanin kowane cewa idan abun da ya fi karfin mutum ya same shi a cikin dare, yana neman makwabta su kawo masa ɗauki, ita kuma ba ta yi hakan ba.

“Da gari ya waye kuma sai ta yi kokarin ta je binne ’yar; don haka dole a sanya mata alamar tamba, in ba haka ba, me take ƙoƙarin ɓoyewa?” in ji shi.

Leave a Reply