Hukumar Lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗi game da halin da asibitoci ke ciki a yankin zirin Gaza, inda rohotanni suka ko ranar Asabar manyan asibitocin yankin biyu sun dakatar da aiki, saboda luguden wuta babu kakkautawa da Isra’ila ke yi da kuma matsalar man fetur.
Babban Daraktan Hukumar Lafiya ta Duniyar Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya yi gargaɗi kan halin da ake ciki na mummunan haɗari ga asibitoci a yankin Zirin Gaza, yana mai cewa ƙarin marasa lafiya, ciki har da jarirai da bakwaini na mutuwa.
Manyan asibitocin Gaza biyu, Al-Shifa da Al-Quds, duk sun rufe, saboda sojojin sari-ka-noƙen Isra’ila na ci gaba da luguden wuta kan duk wani da suka gani kusa da asibitin Al-Shifa, inda dubban mutane suka maƙale a ciki.
KU KUMA KARANTA: WHO ta ce ta kasa tuntuɓar asibitin Al-Shifa na Gaza saboda yanke hanyoyin sadarwa
Ma’aikatar lafiyar Falasɗinu ta bayyana cewa tun a ranar Asabar janareton asibin na karshe ya daina aiki saboda rashin man fetur, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar bakwaini uku da kuma wasu majinyata huɗu. Kuma wasu jarirai 36 na cikin haɗarin mutuwa.
Hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya uku sun bayyana firgici game da halin da ake ciki a asibitocin, inda suka ce a cikin kwanaki 36 an samu aƙalla hare-hare 137 kan cibiyoyin kiwon lafiya a yankin Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 521 da jikkata wasu 686 – ciki har da jami’an kiwon lafiya 16 da suka mutu da kuma jikkatar wasu 38.