Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ya jawo ambaliyar ruwa a sassan Somalia ya sa mutum fiye da rabin miliyan sun tsere daga gidajensu sannan aƙalla mutum 30 sun mutu, a cewar Ministan Watsa Labarai na ƙasar.
Daud Aweis ya bayyana haka ne ga manema labarai ranar lahadi.
Tun farkon watan da muke ciki ake zabga ruwan sama a ƙasar ta Somalia sakamakon sauyin yanayi na El Nino da ke faruwa saboda dumamar ruwa, abin da ya janyo rushewar gidaje sannan ruwa ya shanye gonaki.
Wannan bala’i na faruwa ne a yayin da ƙasar ke ci gaba da fama da fari wanda ya jefa miliyoyin ‘yan ƙasar Somali fuskantar hatsarin kamuwa da tamowa.
KU KUMA KARANTA: Hukumar NEMA ta rarraba kayayyakin agaji ga waɗanda ambaliyar ruwa ya shafa a Kaduna
“Mutum rabin miliyan sun tsere daga gidajensu sakamakon ambaliyar ruwa,” in ji Ministan Watsa Labarai Daud Aweis, inda ya yi gargaɗin cewa lamarin yana iya shafar mutum sama da miliyan ɗaya da dubu ɗari biyu.
Ya ƙara da cewa jami’an gwamnati sun tabbatar da mutuwar mutum 31 ko da yake ya ƙara da cewa “akwai yiwuwar adadin mutanen da suka mutu zai ƙaru”.
Ambaliyar ruwan ta fi yin ɓarna a lardin Gedo da ke kudancin Somalia da lardin Hiran na tsakiya inda Kogin Shabelle ya ɓalle, hanyoyi suka lalace sannan ta rusa gidaje a garin Beledweyne.
Kusan mutum 200,000 ne suka rabu da gidajensu a Beledweyne lokacin da kogin ya ɓalle a watan Mayu.
Somalia na ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi fama da illolin sauyin yanayi kuma ba ta da isassun kayan shawo kan irin wannan matsala.
A makon jiya, Hukumar Bayar da Agaji ta Majalisar Ɗinkin Duniya, OCHA, ta ce ƙasar tana fuskantar “ambaliyar ruwa irin ta mafi muni a tarihi” sannan ta yi gargaɗin cewa tana iya shafar kusan mutum miliyan 1.6.