Daga Haruna Idi Hassan
‘Yan sandan sun kama wata mata mai shekara 51 kan zargin satar wata yarinya ƴar shekara uku a garin Minna na jihar Neja.
Da yake gabatar da wadda ake zargin, kakakin ƴan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun, ya ce a ranar 25 ga watan Oktoba 2023 aka ganta a unguwar Keteren-Gwari tana ƙoƙarin shiga motar haya domin tafiya da wata yarinya ƴar shekara uku da ake zargin an sace ta.
Ya ce ƴan sanda da ke aiki a yankin Tudun-Wada sun kama wadda ake zargin tare da yarinyar kuma da suka yi mata tambayoyi, ta amsa cewar ta sato yarinyar ce daga wani gida a unguwar Tudun-Natsira a ranar da misalin ƙarfe 8 na dare.
KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun sace mata biyar da suka tafi biki a Katsina
Ta ƙara da cewa ta yi niyyar sayar da ita ga wata mata a garin Nnewi da ke jihar Anambara, wadda ta ba ta kwangilar a kan kuɗi N530,000.
Ta ce ta karɓi wasu daga cikin kuɗin N230,000 kafin ta kawo yarinyar da ta sace.
Abiodun, ya ce an mayar da yarinyar ga iyayenta kuma ana ci gaba da ƙoƙarin cafke ɗaya matar da ke Anambara.