Mutum 140 suna jira a zartar musu da hukuncin kisa a Kano

Hukumar da ke kula da gidajen gyaran hali ta jihar Kano a arewacin Nijeriya ta ce mutum ɗari da arba’in ne suke jira a zartar musu da hukuncin kisa bayan kotuna sun same su da laifuka.

Kakakin hukumar, Musbahu Kofar-Nassarawa ne ya bayyana haka ranar Asabar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Nijeriya, (NAN) ya rawaito.

Ya ƙara da cewa mutanen sun haɗa da maza da mata.

“Hukumar da ke kula da gidajen gyaran hali ta Kano ba ta da mai rataye mutane saboda wuri ne na ɗaure mutanen da suka aikata matsakaitan laifuka,” in ji Kofar-Nassarawa.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta dakatar da ƙugiyoyin ƙwadago tafiya yajin aiki da suka shirya

Ya ƙara da cewa gwamnonin da suka mulki jihar sun gaza sanya hannu a takardun zartar da hukuncin kisa ko kuma su mayar da hukuncin na ɗaurin rai-da-rai.

“Wasu gwamnonin suna amfani da damar da ƙundin tsarin mulkin Nijeriya ya ba su domin sakin mutanen da ke kurkuku bisa samun shawarwari daga Majalisar Bayar Da Shawara kan yi wa fursunoni afuwa domin rage cunkoso a gidajen yari,” a cewar Musbahu Kofar-Nassarawa.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *