Yaƙin Gaza: Tinubu ya buƙaci a gaggauta tsagaita wuta

0
185

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya yi ƙira da a gaggauta tsagaita wuta a yaƙin da Isra’ila take gwabzawa da Falasɗinawa a Zirin Gaza.

Ya bayyana hakan ne ranar Juma’a yayin da yake magana a taron Saudiyya da ƙasashen Afirka a Riyadh, babban birnin ƙasar.

Da yake magana a kan taron kuma, Shugaba Tinubu ya ba masu sha’awar zuba jari da cewa Najeriya waje ne mai albarka da ba za su yi da-na-sanu ba muddin suka yi hakan.

Ya kuma buƙaci a ruɓanya alaƙa da Saudiyya domin shawo kan matsalar Boko Haram da ISWAP da ma ta sauran ƙungiyoyi masu tsauraran ra’ayoyi da suka addabi yanƙin Tafkin Chadi da na Sahel.

Tinubu, kamar yadda wata sanarwar da Kakakinsa, Ajuri Ngelale ya fitar ranar Juma’a, ya ce, “Najeriya da Saudiyya sun jima suna hulɗa da juna a matakai daban-daban.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila za ta fara dakatawa da kai hari na tsawon awa huɗu a kowace rana a Gaza — Amurka

“A cikin shekaru 60 da suka gabata, alaƙarmu, wacce a baya ta tsaya a kan iya aikin Hajji, yanzu ta faɗaɗa ta ƙunshi ɓangarori masu yawa.

“Abin farin cikin yanzu shi ne ƙaruwar ’yan ƙasarmu a ɓangarorin lafiya da kwallon ƙafa da dai sauransu.

“Najeriya, kamar Saudiyya, tana aikin faɗaɗa tattalin arzikinta don ya tashi daga mai dogaro da man fetur zalla domin a samu ci gaba. Gwamnatina ta ɗauki wani mataki mai matukar wahala na cire kuɗaɗen ta ake taɓargazarsu wajen biyan tallafin man fetur da kuma daidaita farashin canjin kuɗaɗen ƙasashen waje da sauran manufofin da za su daɗa sauƙaƙa kasuwanci a Najeriya,” in ji sanarwar.

Tinubu ya kuma gode wa gwamnatin Saudiyya saboda bayar da ayyukan jinkai a Najeriya ta hannun Gidauniyar Bayar da Tallafi ta Sarki Salman.

Leave a Reply