No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wani ɗan haya ya shiga hannun hukuma kan zargin yi wa ’yar mai gidan da yake zaune a ciki fyaɗe kuma ta ɗauki juna biyu.

Faston ya shaida wa kotun hukunta laifukan fyaɗe ta Jihar Legas cewa magidancin ya shafe sama da shekara biyu yana lalata da yarinyar, har ta ɗauki ciki ta haihu.

Ya ce abin takaicin shi ne matar ɗan hayan, wadda ma’aikaciyar jinya ce, ta ba wa yarinyar maganin zubar da ciki, don kar asirin mijin nata ya tuno.

“’Yata ta bayyana cewa shi ya yi mata ciki, kuma tun shekarar 2021 yake lalata da ita.

“Na kai ƙara ofishin ’yan sanda, inda ta bayyana musu cewa ya daɗe yana lalata da ita har ta ɗauki cikin da ta haifi ’ya mace.”

KU KUMA KARANTA: An tsare hedimasta kan fyaɗe ga ’yar shekara 4 a makaranta

Ya yi wannan bayanin ne a lokacin da yake amsa tambayoyin lauyan magidancin da ake zargi a gaban kotu.

“Na gamsu cewa shi ne ya yi wa ’yata ciki, kuma matarsa ce ta ba yarinyar maganin zubar da ciki,” inda daga baya ya kai ƙara ofishin hukumta laifukan jima’i.

Kotu ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 11 ga watan Disamba.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...