No menu items!

Sample Page Title

Date:

Ɗaya daga cikin fitattun jaruman shirin fina finan Najeriya a masana’antar Nollywood, John Okafor da aka fi sani da suna ‘Mr Ibu’, ya rasa ƙafarsa sakamakon cutar siga wadda ta sanya likitoci yanke ta domin ceto rayuwarsa.

Ƙasa da wata guda bayan da jarumin ya aike da sako ga jama’ar Najeriya domin ceto lafiyarsa daga barazanar rasa ƙafar, yanzu ta tabbata cewar an yanke ta a asibiti.

A wancan sakon bidiyon da ya aike, Mr Ibu ya nemi taimako da kuma addu’ar ‘yan Najeriya na ceto rayuwarsa, inda yake cewa baya buƙatar ganin an kaiga yanke kafar kamar yadda likitoci suka bada shawara.

Sai dai a litinin ɗin nan, Mr Ibu ya sake gabatar da wata sanarwar dake cewar yanzu ta tabbata an yanke masa ƙafar.

Rahotanni sun ce iyalan gwarzon fina finan ne suka gabatar da sanarwar dake cewa da misalin karfe 1 na ranar litinin aka yankewa mahaifinsu kafa bayan wasu ayyuka guda 7 da likitoci suka masa domin ceto rayuwarsa.

KU KUMA KARANTA: Marasa lafiya sun soma mutuwa, yayin da asibiti ɗaya tilo na cutar kansa a Gaza ya daina aiki

Iyalan sun ce matakin ya girgiza su, amma ya zama wajibi su hakura da aikin domin ceto rayuwarsa.

Daga nan sai suka aike da sakon godiya ga ɗaukacin waɗanda suka taimaka musu wajen ceto rayuwar mahaifin na su, yayin da suka ce Mr Ibu da kansa zai gabatar da na shi godiyar nan gaba.

Daga cikin waɗanda suka kaiwa jarumin fina finan dauki akwai Gidauniyar tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki wadda tace ta biya ɗaukacin kuɗaɗen da ake bukata na jinyar har zuwa ranar 18 ga watan Oktobar da ta gabata.

Mr Ibu na ɗaya daga cikin fitattun jaruman fina finan Nollywood, kuma ya fito a fim sama da 200 da aka naɗa.

Duk da gudumawar da masu sana’ar fina finai ke bayarwa a Najeriya, har yanzu babu wani ingantaccen shiri na kula da rayuwarsu da kuma makomarsu idan sun yi ritaya daga aiki.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...