No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wasu ɓata-gari sun sassari alkalin wata Babbar Kotu ta III (UAC III) da ke Gombe Ayuba Buba Dallas, da wasu mutum uku a garin Degri da ke ƙaramar hukumar Balanga ta jihar Gombe.

Wakilinmu ya ruwaito cewa sai da maharan suka yi wa alkalin da sauran mutane ukun kudan kawo wuka sannan suka sassare su.

Sauran waɗanda lamarin ya shafa sun haɗa da lauya mai suna Barista Usman Yahya da wani ma’aikacin kotu.

KU KUMA KARANTA: Ya je karɓo ‘ya’yansa a wajen tsohuwar matarsa, ‘yan’uwanta sun kashe shi da duka

Wata majiya ta ce wasu mutanen ƙauyen ne suka kai wa alkalin hari a lokacin da suke kokarin ganin sun warware matsalar rikicin wani fili.

Majiyar ta ce alkalin ya sha bugu ne daga ƙauyawan da ba a gane su wane ne ba a lokacin da shi da ma’aikatan kotun suka je duba filin a garin na Degri.

Wasu bayanai na alakanta harin da zargin da wasu ke wa ma’aikatan kotun da neman yin rashin adalci a takaddamar filin.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...