No menu items!

Sample Page Title

Date:

Alfijir Labarai ta rawaito a safiyar wannan Litinin ɗin ce aka wayi gari da tsintuwar gawar wani mai gadi rataye a jikin lilon wata makarantar Firamare da ke Jauro a yankin Tudun Wada na Jihar Gombe.

An dai wayi gari da ganin gawar Malam Abdullahi Ardo a Firamaren mai suna Early Child Care Development Centre da har kawo yanzu ba a gano dalilin rataye kan nasa ba.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Gombe, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ya tabbatar da faruwar da cewa sun samu labarin ne da misalin ƙarfe 8 na safiyar ranar ta Litinin.

A zantawarsa da Aminiya, ASP Mahid, ya ce Abdullahi Ardo Bafulatani ne mai shekara 38 a duniya.

“Bayan mun samu labarin jami’an mu sun je wajen sun ɗauki gawar zuwa asibiti inda likitoci suka tabbatar da mutuwar sa,” inji Mahid.

A cewarsa, yanzu haka suna kan gudanar da bincike domin gano musabbabin da ya jawo ya rataye kansa.

Da wakilinmu ya tuntuɓi Sakataren Ilimi na Ƙaramar Hukumar Gombe, Malam Babuga Audu Dolli, don jin ta bakinsa, ya ce haka kawai aka wayi gari da ganin gawar tasa ba tare da sanin dalilin rataye kansa ba.

Wata majiya ta tabbatar da cewa Malam Abdullahi Ardo ya rasu ya bar Mata da ’ya’ya.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...