An kama tsohon shugaban mulkin sojan Guinea da ya tsere daga gidan yari

0
177

Sojoji sun sake kama tsohon shugaban gwamnatin sojin Guinea Moussa Dadis Camara, bayan ya tsere daga gidan yari da ke Conakry, babban birnin ƙasar Guinea.

A wata sanarwa da ya fitar, babban hafsan sojojin gwamnatin rikon ƙasar Guinea, Janar Ibrahima Sory Bangoura, ya bayyana cewa Moussa Dadis Camara na cikin koshin lafiya kuma yanzu haka ya koma babban gidan yarin da ke birnin Conakry.

Ya ƙara da cewa an kama Kanar Moussa Tiegboro Camara da kuma Kanar Blaise Gomou, da tsere tare da Camara a safiyar asabar, an kuma mayar da su gidan yari kuma ana yin duk abin da ya kamata domin ragowar mutum na karshe da ya tsere, wato Claude Pivi.

KU KUMA KARANTA: ‘Bazoum bai yi yunƙurin tserewa daga Nijar ba’

Blaise Gomou shi ne ministan yaƙi da ta’addacnci a gwamnatin Camara, Claude Pivi kuma  ministan tsaron shugaban ƙasa.

Ma’aikatar shari’ar ƙasar ta sanar cewa Ofishin Antoni-Janar ya ba da umarnin fara shari’a kan manyan laifuka da kae zargin Camara da mukarraban nasa.

A shekarar 2008 ne Moussa Dadis Camara ya yi juyin mulki, zuwa 2010 da aka kifar da shi kuma ya tafi gudun hijira a ƙasashen waje.

A watan Disambar 2021 ya koma Guinea inda daga baya kuma aka zarge shi da mutuwar mutane 150 da jikkata wasu sama da 1,000 a yayin murkushe zanga-zangar da aka yi a Conakry a lokacin mulkinsa a watan Satumbar 2009.

Moussa Dadis Camara, tare da wasu jami’an soji guda biyu, an tsare su a gidan yari da ke yankin Kaloum.

Leave a Reply