Rundunar ƴan sanda ta kama mutane 24 bisa aikata muggun laifuka a Kano

0
237

Kamishinan ƴan sandan jihar Kano CP Muhammad Hussain Gumel ya jinjinawa jami’an sa bisa sadaukarwa wajen yaƙi da masu aikata laifuka daban-daban.

Alfijir Labarai ta rawaito rundunar ƴan sandan jihar Kano ta samu nasarar kama ƙarin wasu mutane 24 da ke ta’ammali da miyagun ƙwayoyi da sauran laififfuka ƙasa da mako guda.

Wananan nasarar na daga cikin umarnin da Babban Sifetan ƴan sandan Nigeria kayode Egbetukun ya bayar wajen gudanar da tsarin inganta mu’amala tsakanin ƴan sanda da al’umma wajen daƙile ayyukan ɓata gari dake tsakanin alumma.

KU KUMA KARANTA: Masu aikata laifuka suna yin shigar matafiya don ƙwace motoci a Nasarawa

A ranar 2 ga watan da muke ciki sashin yaƙi ANTI DABA ƙarƙashin jagorancin O/C Anti-Daba, SP Hussaini Gimba ya samu nasarar kama masu laifin kimanin 24 dake ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.

Ta cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar yace, za a mika manyan dilolin ƙwayar ne ga hukumar yaki da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta NDLEA, domin cigaba da faɗaɗa bincike.

Kamishinan ƴan sandan jihar Kano CP Muhammad Hussain Gumel ya jinjinawa jami’an sa bisa sadaukarwa wajen yaƙi da masu aikata laifuka daban-daban.

Ya kuma buƙaci al’ummar jihar Kano da su ci gaba da baiwa rundunar haɗin kai da goyon baya domin samun nasarar ayyukan ta wajen daƙile ayyukan ɓata gari.

Leave a Reply