Kotun Iran ta yanke wa matar aure hukuncin kisa bisa laifin ‘bin maza’

0
138

Kafofin yaɗa labarai a Iran sun ruwaito cewa kotu a birnin Tehran ta yanke wa wata mata hukuncin kisa bayan kama ta da laifin “cin amanar mijinta.”

Bayanai sun ce mutumin mai suna Parham ya gano cewa matar tasa tana hulɗa da wasu maza ne bayan ya sanya kyamarar tsaro ta CCTV a gidansa.

Ma’auratan biyu sun kwashe shekara 10 a tare.

Mutumin ya ce bayan sanya kyamarori a gidansa sai ya rinƙa ganin wasu maza suna shige da fice a gidan a lokacin da ba shi nan.

A lokacin da aka tuhume ta, matar ta ce ta shiga halin neman maza ne saboda “kaɗaici”, kuma bayanai sun nuna cewa takan gabatar da kanta ga mutane a matsayin mai horas da wasannin motsa jiki.

Ɗaya daga cikin mazan da ta nema ya bayyana cewa “bai ga wata alama da ta nuna cewa matar tana da aure ba.” Kotun ta yanke wa mutumin hukuncin bulala.

Leave a Reply