No menu items!

Sample Page Title

Date:

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu ’yan daudu 8 da suke rawa a wani ɗaurin aure a ƙofar Waika da ke ƙaramar hukumar Gwale a jihar.

Mataimakin babban kwamandan Hisbah, Dakta Mujaheed Abubakar, wanda ya bayyana hakan a ranar Talata, 31 ga watan Oktoba, 2023, ya bayyana cewa an kama waɗanda ake zargin ne bisa ga wata sanarwa daga ‘yan ƙasar da suka nuna cewa samari na sanye da kayan Fulani mata suna rawa a wajen wani biki.

Daga bisani jami’an Hisbah sun kai samame wurin ɗaurin auren, inda suka kama wasu samari takwas ciki har da angon.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Yobe ya rattaɓa hannu kan zartar da hukumar Hisbah da YITDA a jihar

Dakta Mujaheed ya bayyana cewa an gurfanar da waɗanda ake zargin a hukumar Hisbah, inda suka amsa laifin da suka aikata, daga bisani kuma aka gurfanar da su a gaban Kotu.

A martaninsu, waɗanda ake zargin sun roƙi a yi musu sassauci tare da yin alƙawarin ba za su sake yin irin wannan aiki ba.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...