Boko Haram na iya shafe Najeriya idan ba a tashi tsaye ba — Zulum

0
172

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya yi gargaɗin cewa rikicin Boko Haram na iya shafe ƙasar nan idan ba a tashi tsaye don shawo kan shi ba.

Ya yi gargaɗin ne lokacin da yake jawabi bayan ya karɓi baƙuncin kwamitin gudanarwa na Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC) a zauren majalisar dokokin jihar da ke Maiduguri a ranar Litinin.

Ya ce, “Matsayin jihar Borno a taswirar Najeriya yana da matuƙar muhimmanci a gare mu baki ɗaya. Jihar Borno tana da iyaka da Chadi, Kamaru da Jamhuriyar Nijar. Iyakokinmu sun yi yawa don haka tabbatar da tsaro a yankin Arewa maso Gabas ya shafi tabbatar da tsaron ƙasa baki ɗaya.

“Yayin da Arewa maso Yamma da Arewa ta tsakiya da sauran su ke magana kan ’yan fashi, garkuwa da mutane, da sauran su, mu ’yan Boko Haram da ISWAP ne suka addabe mu. Yana da kyau a yi wani abu kafin su mallake jihar.

KU KUMA KARANTA: Babu ƙaramar hukuma ko ɗaya a hanun Boko Haram – Gwamna Zulum

“Dole ne mu dakatar da ɗaukar matasa daga shiga Boko Haram da ISWAP, idan ba haka ba, nan gaba kaɗan, za a shafe duk Najeriya daga taswira,” in ji Gwamna Zulum.

Yayin da yake kokawa kan yawan mutanen da ke gudun hijira, Gwamnan ya ce lamarin na ƙara ta’azzara sakamakon halin matsi da jama’a ke ciki.

“Sannan kuma a Jihar Borno, a 2012, kimanin mutane miliyan 3.5 ne suka rasa matsugunansu. Mun mayar da da yawa amma duk da haka, muna da sama da mutane miliyan ɗaya, mutanen da suka rasa matsugunansu da ke zaune a sansanoni. Wasu na karuwanci, ana shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a sansanonin,” a cewar Zulum.

“Saboda haka muna son hukumar ci gaban Arewa maso Gabas ta shiga tsakani. Muna son ku haɗa kai da gwamnatin jiha domin mu rufe waɗannan sansanonin ‘yan gudun hijira domin mutane su samu abin dogaro da kansu.

“Idan ba haka ba, da yawa daga cikin mutanen za su iya shiga ISWAP da Boko Haram. Waɗannan mutanen da ke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira abu ne mai matuƙar damuwa a gare mu duka. Don haka wannan aiki, na yi wa al’ummar Jihar Borno alƙawarin cewa zan rufe duk wani sansani da ke cikin birnin Maiduguri kuma mun yi hakan da taimakon Allah Maɗaukakin Sarki.

“Yanzu burina na gaba shi ne ganin yadda za mu rufe dukkan sansanonin ‘yan gudun hijira da ke sauran ƙananan hukumomin da babu zaman lafiya.”

Leave a Reply