Muna so gwamnati ta fara biyan mu albashi – masu gadin maƙabartu a Yobe

0
275

Daga Ibraheem El-Tafseer

Masu kula ko kuma masu gadin maƙabartu a jihar Yobe, sun yi ƙira ga gwamnatin jihar Yobe, da ta taimaka ta fara biyansu albashi. Sun yi wannan ƙiran ne a lokacin da Neptune Hausa ta ziyarci wasu daga cikin maƙabartun a garin Potiskum, domin ganin irin yadda ruwa ya mamaye wasu maƙabartun, wanda hakan ya yi sanadiyyar rubzawar ƙabarurruka da yawa a daminar da ta gabata.

Neptune Hausa ta zanta da Malam Adamu Yawale, ɗaya daga cikin masu gadin maƙabartar bayan Asibitin ƙwararru da ke Potiskum (Yobe State Specialist Hospital, Potiskum). Ya shaida wa wakilinmu cewa “A wannan maƙabarta, muna fama da matsaloli, musamman na rubzawar ƙaburbura, kuma babu ƙasar cuko. Muna so gwamnati ko wasu al’umma su taimaka su kawo mana ƙasa don mu cike ƙaburburan da suka rubza.

Sannan muna tsananin buƙatar itace na buso a wannan maƙabarta. Lokuta da dama sai an kawo za a binne mutum, amma babu itacen da za a saka kabari wanda za a binne mutum da shi. Dole sai dai ‘yan’uwan mamacin su fita su je su sayo itacen, kafin a binne mutum”.

KU KUMA KARANTA: Tinubu ya ba da umarnin biyan malaman jami’a albashin watannin da suka yi suna yajin aiki

Malam Adamu, ya ƙara da cewa “kullum a wannan maƙabarta muke wuni. Mune muke kula da ita, mune muke tona ƙaburburan da ake zuwa ake binne bayin Allah. Ba ma samun abin kashewa, da na cefane ga iyalanmu, sai dai idan an kawo jana’iza, idan jama’a sun taimaka mana da sadaka, sannan muke samun ɗan wani abu”.

Malam Sulaiman Sa’id, ɗaya ne daga cikin masu gadin maƙabartar Mamman B. Ali, wadda aka fi sani da maƙanartar MAL. Ya shaida wa wakilinmu cewa “wannan maƙabarta, ta fi kowace maƙabarta girma a garin Potiskum. Amma duk girmanta wannan maƙabarta, ba ta da hanyar ruwa, ka ga kuwa idan wuri ya yi girma kuma babu hanyar ruwa, to dole ne wurin ya nashe. Ta haka yake samun dama ya je ya shiga kabarurruka, ya rubzasu. Duk kyan aikinku a wannan maƙabarta, sakamakon rashin hanyar ruwa, sai ruwan ya je ya rusa kabarurruka.

Babban abin da muke buƙata shi ne gwamnati ta zo ta cire mana hanyar ruwa guda biyu ko uku, wanda ruwan zai samu hanyar fita waje. Sannan muna tsananin buƙatar itace a wannan maƙabarta. Kusan dukkan ƙauyukan kusa damu, nan maƙabartar suke kawo jana’iza. Ana kawo jana’iza 20 zuwa 30 a kullum a wannan maƙabarta. To wannan ne yake sa wa duk yawan itacen da aka kawo wannan maƙabarta yake yawan ƙarewa. Babu shakka jama’a suna taimaka wa da itace, amma yawan jana’iza da ake kawo wa, shi ne yake kawo ƙarewar itacen da wuri.

Sannan buƙata ta gaba shi ne, muna so gwamnati ta fara biyanmu albashi. A iya sanina, a dukkan maƙabartu na garin Potiskum, waɗanda gwamnati take iya biyansu albashi, mutane biyu ne. Gwamnati ba ta biyan mutanenmu masu kula da dukkan maƙabartu kuɗi don su dinga ciyar da iyalansu. Muna so gwamnati ta dube mu da idon rahama, ta dinga biyanmu albashi, don mu dinga samun abin da za mu ciyar da iyalanmu”. inji shi.

Leave a Reply