Gwamnatin Zamfara ta ba da umarnin rufe kasuwar Maru, bayan harin ‘yan bindiga a garin

0
180

Wasu ‘yan bindiga da dama sun kai hari fadar Sarkin Maru Abubakar Gado Maigari inda suka kashe wani mai gadin fadar a daren Laraba.

‘Yan bindigan sun sake komawa fadar a daren Alhamis da nufin kashe ko kuma sace sarkin, amma suka kai farmaki kan jama’ar da ba su ji ba, ba su gani ba lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane huɗu.

Sarkin da ƙyar ya tsallake rijiya da baya a harin da ‘yan bindigan suka kai a ranar Laraba da Alhamis da daddare, in ji wata majiya.

An tattaro cewa ‘yan ta’addan sun yi yunƙurin yin garkuwa da Sarkin bai yi nasara ba, inda suka riƙa kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a lokacin da suka je gida gida suna neman mazauna garin da nufin yin garkuwa da su.

KU KUMA KARANTA: Mummunan harin da sojojin suka kai a Sakkwato, ya kawo ƙarshen ‘yan ta’adda da dama a jihar

Harsashin bindiga da dama ya janyo hasarar ababen hawa da wasu kayayyaki masu daraja, sannan kuma an jikkata wasu mutanen yankin da ba a san adadinsu ba a yayin aikin.

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal a wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai Munnir Haidara ya sanyawa hannu ya yi Allah wadai da harin tare da bayyana shi a matsayin dabbanci da rashin mutuntaka.

Gwamnan ya kuma bayar da umarnin rufe kasuwar Maru, ba tare da ɓata lokaci ba, har sai an daidaita matsalar tsaro a ƙaramar hukumar.

Manufar ita ce a wargaza duk wani shiri na ta’addanci na kai wa mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba a kasuwa hari, tare da samar da ƙarin na’urori da za su taimaka wa gwamnati da hukumomin tsaro wajen yaƙar masu aikata laifuka.

A farkon shekarar nan ne aka kai hari a hedikwatar ‘yan sanda da ke ƙaramar hukumar Maru, kuma an kashe wani DPO da wasu jami’ai a wani shingen bincike na ‘yan sanda.

An yi jana’izar waɗanda ‘yan bindiga suka kashe a ranar Juma’a da rana a ƙaramar hukumar Maru.

Har yanzu dai hukumomin ‘yan sanda a Zamfara ba su ce uffan ba kan lamarin.

Leave a Reply