Sojojin Amurka sun kai hare-hare ta sama a Syria

0
156

Sojojin Amurka sun ce sun kai hare-hare ta sama a wurare biyu da sojin juyin-juya-hali na Iran ke amfani da su a Syria.

A wata sanarwa da Sakataren Tsaron Amurka ya fitar Lloyd Austin, ya bayyana hare-haren na tsantsar kare kai.

Lloyd Austin ya ce martani ne ga jerin hare-haren da ƙungiyoyin da ke samun goyon bayan Iran suka fara kai wa dakarunta tun daga ranar 17 ga wannan wata na Oktoba.

Sun ce martani ne kan hare-haren da suke addabar sojin Amurka da ke Iraqi da Syria hare-hare.

Sama da mako guda da rabi kenan da sojin Amurka ke zafafa kai hare-hare kan ƙungiyar masu ɗauke da makamai da Iran ke marawa baya.

Ma’aikatar Tsaro ta Pentagon ta ce an kai wa ƙawancen da Amurka ke jagoranta a Iraqi da Syria hari sama da sau 16 cikin wannan watan.

KU KUMA KARANTA: Sojojin Pakistan tara sun mutu, sakamakon hare-haren ‘yan Taliban

Sanarwar ta ce sai da ta aike da saƙo ga shugaban addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei a game da hare-haren da ake kai wa dakarun ƙasar a Gabas Ta Tsakiya a daidai lokacin da ake zaman ɗar-ɗar a yankin Gabas ta Tsakiya saboda yaƙin Isra’ila a Gaza.

Amurka ta ce wannan mataki da ta ɗauka a kan Iran da ƙungiyoyin da take mara wa baya a Syria ba shi da nasaba da Isra’ila, hasali ma ba ta tuntuɓi Isra’ilar ba kafin ɗaukar sa.

Leave a Reply