Adadin mutanen da suka rasa muhalli a sassan duniya ya zarta miliyan 114 — MƊD

0
185

Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa, adadin mutanen da suka rasa muhallansu a sassan duniya ya zarta miliyan 114, adadi mafi girma da majalisar ta tattara a tarihi.

Babbar matsalar da ta raba mutanen da gidajensu a watanni shida na farkon wannan shekara ta 2023, ita ce tashe-tashen hankulan da ake fama da su a Ukraine da Sudan da Somalia da Myanmar da Jamhuriyar Dimokuraɗiyar Congo har ma da rikici a Afghanistan.

Kazalika ibtila’o’in da aka samu na fari da ambaliyar ruwa da rashin tsaro sun taimaka wajen raba mutanen da gidajensu kamar yadda Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijra ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNHCR) ta bayyana.

Sanarwar UNHCR ta ce, yanzu haka hankalin duniya ya karkata ne kan yaƙin da ake fama da shi a Zirin Gaza wanda ya cika da ɗimbim fararen hula, amma fa akwai rikice-rikice da dama da ke ci gaba da ta’azzara tare da raba mutane da muhallansu a sassan duniya.

KU KUMA KARANTA: Ta nemi Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙaddamar da yaƙi kan yin hijira ba bisa ƙa’ida ba

Shugaban hukumar, Filippo Grandi ya zargi ƙasashen duniya da gazawa wajen magance tashe-tashen hankula da dama, yana mai buƙatar samar da haɗin kai don kawo ƙarshen matsalar ta raba mutane da muhallansu tare da komar da su gida.

Grandi ya kuma ce, wani kaso na adadin mutane da suka rasa muhalli sun tsere daga gidajensu ne sakamakon matsalar take haƙƙin ɗan Adam da ake fama da ita a wasu sassan.

“Gazawar al’ummomin duniya wajen magance rikice-rikice ko hana aukuwar sabbi shi ne musabbabin rasa muhalli da kuma ƙara jefa waɗanda lamarin ya shafe cikin zullumi.

“Dole ne mu yi wa kanmu karatun ta nutsu, mu yi aiki tare don kawo ƙarshen rikice-rikice, wanda hakan zai bai ’yan gudun hijira da sauran mutanen da suka rasa matsugunansu su koma gida ko kuma su sake gina matsugunansu,” in ji Grandi.

Ya zuwa watan Yuni, adadin mutanen da aka tilastawa gudun hijira a duniya ya kai miliyan 110, wanda wannan wani ƙari ne kan mutum miliyan 1.6 da suka tsere daga muhallinsu a rahoton da aka fitar a ƙarshen shekarar 2022.

Haka kuma, a tsakanin watan Yuni zuwa ƙarshen watan Satumba, an ƙiyasta ƙarin wasu miliyan huɗu da aka tilastawa gudun hijira, wanda ya kawo adadin zuwa miliyan 114.

Rahoton na UNHCR bai ƙunshi alƙaluman rikicin Isra’ila da Falasɗinu ba wanda ya ɓarke a ranar 7 ga Oktoba ba.

Leave a Reply