No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wani Supritanda na ‘yan sanda Nahun Gwadi Eli ya mutu a ɗakinsa na otel dake Jos babban birnin jihar Filato.

An tsinci gawar jami’in ne a ƙasa a gefen gadonsa bayan da jami’an da abin ya shafa suka fasa ɗakin otal ɗinsa a ranar 23 ga Oktoba, 2023.

Har zuwa rasuwarsa, Eli shi ne Kwamandan A/O SWAT, Rundunar Jihar Filato.

A cewar majiyoyi, mutanen nasa sun shiga cikin damuwa bayan da suka yi ta ƙiran layin wayarsa ba tare da amsa ba.

’Yan sandan sun nufi ɗakinsa na otal inda suka yi ta ƙwanƙwasa sau da yawa, amma ba su samu amsa ba.

 Sai da suka buɗe ƙofar ɗakin otal suka same shi ya mutu.
An ɗauke gawarsa zuwa ɗakin ajiye gawa na asibitin Jos domin gudanar da bincike.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...