’Yan bindiga sun kashe limami sun sace uwa da ’ya’yanta a Kaduna

0
134

’Yan bindiga sun kashe limami da wani mutum guda a cikin masallaci a yankin Ga-Allah da ke gundumar Kakangi a ƙaramar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna.

Sa’o’i kaɗan bayan nan kuma ’yan bindiga suka kashe wani ɗan banga wani magidanci, suka yi awon gaba da matarsa da ’ya’yansa bayan sun jikkata wasu mutum uku a cikin garin Birnin Gwari.

Shugaban Kwamitin ci gaba da samar da tsaro a Birnin Gwari, Ibrahim Abubakar Nagwari, ya bayyana cewa ’yan bindigar sun sace mutane da dama a harin na biyu da suka kai da magariba a gidan mai a yankin Bagoma Dam da ke cikin garin.

“An kashe wani ɗan banga (Mu’awiyya) da wani ɗan gudun hijira daga ƙauyen Dagara, da wasu mutum uku kuma sun samu rauni, amma suna samun sauƙi a Babban Asibitin Jibrin Maigwari da ke Birnin Gwari,” in ji shi.

Ya bayyana cewa ko kafin jami’an tsaro su zo su yi wa yankin ƙawanya, ’yan bindigar sun riga sun tsere.

KU KUMA KARANTA: An kama waɗanda ake zargi da kashe wata mata, ta hanyar yi mata yankan rago a Gwambe

Wani mazaunin yankin mai suna Muhammadu, ya shaida mana cewa da ’yan bindigar suka fice daga Bagoma sai suka far wa Anguwar Shakaru, inda suka kashe wani matsahi, suka yi awon gaba da matarsa da ’ya’yansa.

Shugaban ƙungiyar ci gaba Masarautar Birnin Gwari (BEPU) Ishaq Kasai ya bayyana damuwa kan harin da aka kai gidan man na KBY.

An ruwaito wani basaraken yankin na Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Abdulrauf, yana roƙon gwamnati ta ƙaro tura jami’an tsaro a sassan ƙaramar hukumar.

Ya kuma roƙe ta da ta ba wa jama’a izinin ɗaukar bindiga don kare kansu, lura da yadda ’yan bindigar ke ƙara tsaurin ido suna shigowa har cikin gari su kawo hari.

Wakilinmu ya yi ƙoƙarin samun ƙarin bayani daga kakakin ’yan sanda na Jihar Kaduna, Officer ASP Mansir Hassan amma haƙarsa ba ta cim-ma ruwa ba.

Ya ƙira wayar jami’in, amma bai amsa ƙiran ba, haka ma rubutaccen saƙon da aka tura masa babu amsa.

Leave a Reply