Jami’an tsaro sun kama bindigogi 150 a gidan ɗan ta’adda a Neja

Jami’an tsaro sun gano bindigogi ƙirar AK-47 kimanin 150 da albarusai sama da 3,000 a gidan wani ɗan bindiga da suke nema ruwa a jallo a jihar Neja.

Majiyoyi sun ce an yi ɗauki ba daɗi tsakanin ɗan bindigar da jami’an tsaro na tsawon sa’o’i a daren Talata, a unguwar Gbeganu da ke Minna, babban birnin jihar, inda suka gano bindigogin da harsasai sama da 3,000.

Wata majiyar tsaro ta shaida wa wakilinmu cewa makaman da aka kama a gidan ɗan bindigar sun haɗa da bindigogi ƙirar AK-47 guda 150, bindiga ƙirar AA, albarusai 3,000, makamin roka, da kuma abubuwan fashewa.

Mazauna yankin sun ce sun shiga tashin hankali da jin musayawar wutar da aka fara da misalin ƙarfe 12 na dare, kafin ɗan bindigar ya tsere.

Sun bayyana cewa wanda ake zargin ya yi amfani da makamin roka ya rusa wani ɓangare na gidan nasa, inda ta nan ya samu ya tsere, amma jami’an tsaro sun kama matarsa ’ya’yansa da ke gidan.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun yi artabu da gungun masu aikata laifuka, sun ƙwato bindigogin guda biyu

Majiyarmu ta ce ganin jami’an tsaro ta na’urar CCTV ke da wuya, sai ɗan ta’addan da suka je nema ya buɗe musu wuta, su kuma suka mayar da martani.

Wani mazaunin unguwar ya shaida wa wakilinmu cewa, “gaskiya ba mu yi barci ba, saboda ƙarfin ƙarar harbe-harben, yadda ka san bom ake harbawa.

“Ta ƙofar gidanmu jami’an tsaron suka wuce a lokacin da za su gidan, ba mu san inda suka nufa ba, sai daga baya muka fara jin harbe-harbe.”

Ya bayyana cewa harsashi ya samu wani mai gadi a ayin musayar wutar, inda aka kai shi Asibitin ƙwararru Ibrahim Badamasi Babangida domin ba shi kulawa.

A lokacin da wakilinmu ya je yankin a safiyar Talata, ya ga wasu bangayen gidan sun faɗi, ƙofa da bango da kuma tagogin gidan kuma da ruwan harsasai a jikinsu.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *