Daga Ibraheem El-Tafseer
Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Mai Mala Buni CON, ya samu baƙin labarin rasuwar jigo, dattijon jiha, kuma fitaccen ɗan jihar Yobe Malam Adamu Fika (Wazirin Fika).
Gwamna Buni ya bayyana rasuwar Wazirin Fika a matsayin babban rashi ne a ƙasa, ba iya al’ummar jihar Yobe kaɗai ba. Muna miƙa ta’aziyya ga iyalansa, Masarautar Fika, da jihar Yobe.
“Mun yi rashin babban shugaba, mai ba da shawara mai hikima, abin alfahari ga jiharmu, kuma mai kishin gaskiya da adalci.
“Rasuwar Malam Adamu Fika ta rufe ƙofar tuntuɓa ga gwamnatinmu tare da kawo cikas wajen karɓar bashi daga tarin ƙwarewa na gogaggen mai fasaha kuma gogaggen ma’aikaci,” in ji Gwamna Buni.
“Ina fata, a madadin kaina, gwamnati da al’ummar Jihar Yobe, ina jajantawa iyalansa da Masarautar Fika.
KU KUMA KARANTA: Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, ta yi alhinin rasuwar Malam Adamu Fika
“Ina roƙon Allah (T) Ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma sa ya huta a Aljannatul Firdaus.
“Ina kuma roƙon Allah Maɗaukakin Sarki da Ya baiwa iyalansa da Masarautar Fika ƙwarin guiwar jure wannan babban rashi da ba za a iya maye gurbinsa ba” Gwamna Buni ya yi addu’a.