Najeriya za ta ɗauki mataki a kan masu hana ’yan ƙasarta biza

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa daga yanzu za ta mayar da martani a kan duk ƙasar da take ƙin bai wa ‘yan ƙasar takardar izinin shiga ƙasarta.

Bayanai sun ce dai ta kama hanyar cimma ruwa domin bayan kwashe shekaru ne ana muzgunawa ‘yan Najeriyar da ke neman takardun biza na shiga ƙasashen duniya ne gwamnatin Najeriyar ta ɗauki wannan mataki.

Ministan kula da harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo dai ya bayyana cewa lokaci ya wuce da Najeriyar za ta rinƙa bai wa ‘yan wasu ƙasashe izinin ziyarar ƙasar amma kuma a yi wa ƙasar ƙememe.

Ministan ya ce daga yanzu Najeriyar za ta maida martani.

Ana iya tuna cewa, tun a watan Oktobar bara ne Gwamnatin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta sake haramta wa ’yan Najeriya ziyartar ƙasarta ba tare da bayyana dalilinta na ɗaukar wannan tsauttsauran mataki ba.

KU KUMA KARANTA: Masar ta buɗe iyaka ga ‘yan Najeriya da suka tsere daga Sudan

Ƙasar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta rarraba wa abokan hulɗar kasuwancinta daga Najeriya da suka haɗa da ejan-ejan da ke samar wa ’yan ƙasar takardun biza, matakin da ake ganin zai daɗa dagula rikicin diflomasiya tsakanin ƙasashen biyu.

Wannan na zuwa ne bayan ’yan makonni da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta tsaurara matakan bayar da biza ga sabbin baƙin da ke marmarin shiga cikin ƙasar.

Sanarwar ta ce, hukumomin ƙasar sun soke ɗaukacin buƙatun neman takardun biza daga ’yan Najeriya da wasu ƙasashen Afirka na baƙaƙen fata.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *