Hukumar Kula Da Ingancin Makarantu ta Jihar Kaduna ta rufe makarantar Al-Azhar da ke Zariya kan zargin kashe wani ɗalibi da duka.
A ranar Asabar ne aka bayar da rahoton mutuwar wani ɗalibi ɗan aji uku a sakandare wanda ya rasu kan zargin duka mai tsanani da wasu malamai suka yi masa har suka cire masa haƙora.
Rahotanni sun ce malaman sun zane yaron ne bayan ya daina zuwa makaranta na wasu kwanaki sakamakon an buƙaci ya maimaita aji bayan ya faɗi jarabawar zuwa aji na gaba.
Cikin wata sanarwa da darakta janar na hukumar ta KSSQAA, Dakta Usman Abubakar ya fitar a ranar Lahadi, ta ce Ma’aikatar Ilimi ƙarƙashin wakilcin gwamnatin jihar ta ƙaddamar da bincike kan lamarin.
KU KUMA KARANTA: An kashe ɗalibi da duka a makarantar Al-Azhar Academy da ke Zariya
Ya bayyana cewa sun kai ziyara zuwa Zariya domin tattara bayanai kan haƙiƙanin abin da ya faru a makarantar Al-Azhar Academy wanda a nan lamarin ya faru da gidan su mamacin domin yin ta’aziyya ga iyalansa da wasu abokan karatunsa.
Haka kuma Abubakar ya bayyana cewa sun kai ziyara hedikwatar ‘yan sanda a Zariya wanda a nan ne shugaban makarantar da mataimakinsa ke tsare.
Haka kuma shugaban hukumar ta KSSQAA ya ce sun kai ziyara maƙabartar da aka binne yaron.
Ya kuma bayyana cewa makarantar ta Al-Azhar za ta ci gaba da zama a rufe har sai abin da bincike ya nuna.
Sanarwar ta kuma yi ƙira ga al’umma da su kwantar da hankulansu, tare da bin doka da oda, yayin da ta ce ma’aikatar ilimin jihar na ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, domin tabbatar da gaskiya da adalci.
Wakilinmu ya ziyarci gidan iyayen ɗalibin da ya rasu, wato gidan Alhaji Sambo da ke unguwar Kofar Kuyambana cikin birnin Zariya.
Isa Sa’idu, ɗaya ne daga cikin iyalan da ya bayyana mana yadda lamarin ya faru inda ya ce, “A jiya da safe abokin mahaifin marigayi ya ɗauke shi zuwa makarantar sakamakon marigayin ya daina zuwa, wai saboda an koma da shi ajin baya don haka ya ce baya son makarantar.
“Wanda ake zargi da aikata kisan ya ce ya damƙa marigayin a hannun Mataimakin Shugaban makaratan, kuma ya ce tun a gabanshi ya fara dukan marigayin.”
‘An yi masa bulala sama da 100’
Malam Isa, ya ƙara da cewa a bayanin da suka samu daga abokan karatun ɗalibin a makarantar shi ne an gabatar da shi a gaban ɗaliban aka yi masa bulala kusan 100, daga nan kuma aka kai shi ofishin Shugaban Makarantan, inda a nan ma aka sake tuɓe masa riga aka ci gaba da dukan shi har sai da wasu daga cikin haƙoransa suka fice daga bakinsa.
Daga nan da suka ji ba ya numfashi sai suka kai shi hanyar banɗaki suka shimfidar da shi, sannan suka kai shi asibiti.
Bayanan da wakilinmu ya samu na nuni da cewa duk da mutuwar wannan ɗalibi, mahukuntar makarantar ba su sanar da iyayensa ba har sai da iyayen yaron suka riƙa jin raɗe-raɗin cewa an kai shi asibitin Al-Ridha Clinic da ke kusa da makarantar.
“A nan ne suka garzaya asibitin domin su tabbatar da gaskiyar labarin. Da isar su asibitin sai likitan da ya duba yaron ya tabbatar musu da cewa shi ne ya duba yaron, kuma gawa aka kawo musu, ba marar lafiya ba,” in ji Isa.
Da wakilinmu ya ziyarci makarantar domin tabbatar da gaskiyar lamarin, ya tarar da makarantar a kulle.
Sai dai mun zanta da wasu daga cikin ɗaliban makarantar da suka kai ziyarar ta’aziyya gidan abokin karatun marigayin.
Ɗaya daga cikin yaran wanda suke aji ɗaya da ɗalibin kuma muka sakaya sunansa, ya ce, “Mataimakin Shugaban Makarantar shi ya zo da yaron gaban “Assembly” inda suka riƙa yi masa bulala babu ƙaƙƙautawa tare da Shugaban Makarantar, tun muna iya ƙirga bulalar har muka ɓata lissafi, ko ni na ƙirga bulala aƙalla 105 wanda aka yi wa marigayin a gabanmu,” in ji ɗalibin.
“Daga nan kuma suka wuce da shi zuwa ofishin Shugaban makarantar, suka cire masa riga, suka bar shi da gajeren wando kawai suka ci gaba da dukansa har yaron ya yi yunƙurin guduwa, amma aka sa shuwagabannin ɗaliban makarantar suka riƙe shi suka koma da shi, aka ci gaba da dukansa har sai da suka cire masa haƙora, suka kashe shi,” in ji shi.
‘A kan rashin zuwa makaranta aka yi masa hukuncin’
An gano cewa ana zargin an yi wa ɗalibin hukuncin ne saboda ɗalibin ba ya son zuwa makaranta kullum saboda kunya da yake ji na komawa da shi ajin baya da aka yi masa sakamakon rashin yin ƙoƙari a aji.
“Bayan sun kashe Marwanu sai suka fito da gawar waje, suka ajiye shi a hanyar zuwa banɗaki har aka tashi makaranta,” in ji ɗalibin.
Sai dai har zuwa lokacin da wakilinmu ya ziyarci gidan mahukuntan makarantar ba su ziyarci iyalan mamacin ba domin jajanta musu.