Indiya ta ba wa Falasɗinawa kayan jinƙai

0
173

Indiya ta tura ton 38.5 na kayan abinci da magunguna da sauran kayan jinƙai ga al’ummar Falasɗinawa da hare-haren Isra’ila suka daidaita a Zirin Gaza.

A safiyar Lahadi Indiya ta tura jirgin sojinta ɗauke da kayan zuwa yankin Sinai na ƙasar Masar, inda daga nan za a tsallaka da su zuwa Zirin Gaza.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Indiya, Arindam Bagchi, ya ce kayan sun haɗa da “tantuna da shinfiɗu da mayafai, da sabulai na sinadaran tsaftace ruwa da tampol da dai sauransu”.

Ranar Asabar aka fara shigar da kayan jinƙai ga Falasɗinawa ta mashigar Rafah da ke ƙarƙashin kulawar ƙasar Masar, ta hannun ƙungiyar jinƙai ta Red Crescent.

Ƙungiyar ta bayyana rukunin farko na motoci 20 da suka fara shiga yankin Zirin Gaza a matsayin abin da bai kai cikin cokali na kayan agaji da ake buƙata a yankin ba.

KU KUMA KARANTA: Motocin kayan agaji sun fara shiga zirin Gaza

Isra’ila ta kashe Falasɗinawa sama da 4,300 akasarinsu fararen hula, mata da ƙananan yara da tsofaffi a Zirin Gaza, inda ta jikkata wasu 13,000 a makonni biyu da ta kwashe tana wa yankin luguden wuta.

Sama da mako guda ke nan da Isra’ila ta yanke wa Zirin Gaza ruwan sha da wutar lantarki da hanyoyin sufuri tare da hana shiga da fita a yankin, da sunan samame don murƙushe ƙungiyar Hamas.

A makon jiya ta kai hari da ya hallaka fararen hula kimanin 500 a wani asibiti da ke Kudancin Zirin Gaza, bayan da ta umarci Falasɗinawa da su koma yankin da zama.

Sama da Falasɗinawa miliyan ɗaya ne jiragen Isra’ila suka yi ruguje gidajensu a Zirin Gaza, yankin da ke da mazauna kimanin miliyan 2.4.

Isra’ila wadda sojojinta ke shirin kutsawa cikin Zirin Gaza ta kasa ta ƙaddamar da hare-haren jiragen ne bayan ƙazamin harin da ƙungiyar Falasɗinawa ta Hamas ta kai mata, inda mayaƙan ƙungiyar suka kashe mutum 1,400 suka yi garkuwa da wasu kimanin 200.

Indiya ta yi tir da harin na Hamas, amma ta jaddada buƙatar kafa ƙasar Falasɗinawa mai cikakken ’yanci.

Leave a Reply