Sojoji sun kashe mayaƙan ISWAP shida a jihar Borno

0
201

Dakarun sojin Najeriya sun kashe mayaƙan ISWAP shida tare da fatattakar wasu da dama a wani harin kwantan ɓauna da ƙungiyar ta kai musu suna sintiri a unguwar Binduldul da ke kan hanyar Maiduguri-Gubio-Kareto-Damasak.

Sojojin da aka girke a Damasak sun yi musayar wuta da ’yan ta’addan suka tsere cikin daji, kamar yadda wata majiyar leƙen asiri ta shaida wa Zagazola Makama, wani mai sharhi kan harkokin tsaro kuma ƙwararre kan yaƙi da ta’addanci a yankin tafkin Chadi.

KU KUMA KARANTA: Sojoji sun kashe ‘yan fashi 10 tare da ceto mutane tara a Zamfara

Majiyar ta ƙara da cewa, sojojin sun shiga cikin dajin domin fatattakar ’yan ta’addar, kuma a yayin arangamar mayaƙan ISWAP da ba a tantance adadinsu ba sun samu raunuka.

Sojoji 3 ne suka samu raunuka a yayin arangamar, yayin da aka ƙwato bindigogin PKT guda biyu, AK-47 guda biyar, da motar bus ƙirar Hummer guda ɗaya da ’yan ta’addar ke amfani da su.

Leave a Reply