No menu items!

Sample Page Title

Date:

Aƙalla mutane takwas ne suka rasa rayukansu yayin da ’yan fashi da makami suka kai hari kan wasu bankuna a yankin Otukpo da ke Jihar Benuwe.

Wakilinmu ya ruwaito cewa tsautsayin ya rutsa da bankuna huɗu da suka haɗa da UBA, Stanbic, First Bank da Zenith.

Cikin waɗanda suka rasa rai akwai ’yan sanda 3, ɗan sintiri ɗaya, wani kansila a yankin da kuma masu hulɗa da banki guda biyu.

Rahotanni sun bayyana cewa sai da ɓarayin suka kai farmaƙi kan ofishin ‘yan sanda da ke daura da bankunan kafin samun damar aukawa cikin bankunan.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kai hari gidan ɗan majalisa a Kwara, sun tafi da matarsa da ‘ya’yansa

Aƙalla sun shafe sa’a ɗaya suna sata kafin ficewa daga yankin suna harbin iska a motocin Hilux biyu da wata ƙaramar mota ɗaya.

Kakakin rundunar ’yan sanda, SP Catherine Anene ta tabbatar da aukuwar al’amarin, sai dai ta ce ba ta da cikakken bayani a kai.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...