No menu items!

Sample Page Title

Date:

Ma’aikatan filin jiragen sama na Malam Aminu Kano da ke Kano sun gudanar da zanga–zangar lumana don nuna rashin gamsuwarsu da wani gini da Rundunar Sojin Sama take yi a gaban gidajensu.

Sojojin dai na yin gine-ginen ne a gaban gidajen nasu da ke rukunin gidajen na ma’aikatan filayen jiragen sama da ke Kano, wato Aviation Quarters.

Shugaban Harkokin Tsaro da Walwalar Ma’aikatan, Kwamared Muhammad Zakariyya Dauda ya ce sun wayi gari sun ga sojojin sun mamaye unguwar tasu tare da yi musu gini a filin da suke motsa jiki su da ’ya’yansu.

“Muna wajen aiki ne ’yan uwanmu da ke gida suka yi mana waya cewa sojoji sun yi mana kutse a gidajenmu tare da fara gini a filin da ke cikin gidajenumu.

KU KUMA KARANTA: An yi wa ‘yan sanda biyar duka a Abuja, a ƙoƙarin ceton wanda ake zargi da satar mazakuta

“Wannan fili shi ne muke amfani da shi wajen motsa jiki mu da ’ya’yanmu. Ba su tuntuɓe mu ba suka cire mana allon da ke ɗauke da sunan hukumarmu a jiki.”

Haka kuma ma’aikatan sun zargi sojojin da hana su shiga gidajensu tare da dukan wani daga cikinsu a daidai lokacin da yake ƙoƙarin sauƙe ’ya’yansa da ya ɗauko daga makaranta.

“Waɗannan sojojin sun hana ma’aikatanmu shiga gidajensu har ma suka sa kan bindiga suka doki wani ma’akacinmu a lokacin da yake ƙoƙarin shiga unguwar don sauƙe ’ya’yansa da ya ɗauko daga makaranta,” in ji Kwamared Muhammad.

Har ila yau, ma’aikatan sun nemi Shugaban ƙasa da Majalisar ƙasa da duk masu ruwa da tsaki da su sanya baki cikin lamarin don ganin an yi wa tufkar hanci.

Kakakin Rundunar Sojin Sama Air commodore Edward Gabkwet, ya ce zai bincika tare da sanar da manema labarai halin da ake ciki. Amma har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton bai tuntuɓe mu ba.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...