No menu items!

Sample Page Title

Date:

Harin da Isra’ila ta kai a Cocin Saint Porphyrius Greek Orthodox a Gaza ya kashe mata a ƙalla biyu sannan ya jikkata fararen-hula da dama, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Falasɗinu (WAFA) ya rawaito.

Ma’ikatar Harkokin Cikin Gida ta Falasɗinu ta ce mutane da dama sun mutu yayin da wasu suka jikkata sakamakon harin, wanda ta bayyana a matsayin “sabon kisan kiyashi”.

Ma’aikatar ta ƙara da cewa mutane da dama da hare-haren Isra’ila suka kora daga gidajensu ne suke samun mafaka a cocin lokacin da jiragen yaƙin Isra’ila suka kai harin.

Mutane da dama “sun yi shahada yayin da wasu suka jikkata” a harin da Isra’ila ta kai cocin, in ji ma’aikatar.

KU KUMA KARANTA: Iran ta gargaɗi Isra’ila kan ci gaba da kai hari kan Falasɗinawa

Ganau sun ce harin ya lalata ƙofar shiga cocin da wasu gine-gine da ke daura da shi, suna masu ƙara wa da cewa an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti.

Abu Selmia, darakta janar na Asibitin Shifa, ya ce an jikkata gomman mutane a harin da Isra’ila ta kai Cocin Saint Porphyrios ko da yake bai bayyana takamaiman yawan mutanen da suka mutu ba da waɗanda gini ya rufta a kansu ba.

Wani da ya tsira daga harin ya shaida wa gidan talabijin na Al Jazeera Arabic cewa sojojin Isra’ila ba su aika musu da gargaɗin fice wa daga cocin ba kafin kai harin.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...