No menu items!

Sample Page Title

Date:

A wani rahoto da muke samu ya tabbatar mana cewa ɗaruruwan al’ummar ƙasar falasɗinune suka gabatar da sallar juma’a a harabar babban masallacin na uku cikin manyan masallatai na addinin musulunci.

Bugu da ƙari sun gabatar da sallar ne a gaban masallacin duk da barazana na dakarun sojojin yankin Isra’ila.

Idan za a iya tunawa ana ci gaba da zaman doya da manja tsakanin dakarun musulunci na Hamas da kuma dakarun sojin Isra’ila da ke ƙoƙarin mamaye Gaza ko ta wanne hali, lamarin da ya sa ‘yan Hamas da dakarun Hizbullah ke ci gaba da yiwa Isra’ila ɓarin wuta duk da harin ramuwar gayya da isra’ilan ke kai wa muhimman wurare a Gaza.

Yanzu haka dai tuni dandazon falatsɗinawa suka gabatar da sallar juma’a tare da gabatar da addu’o’i domin neman kariya daga Allah (T).

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...