’Yan sanda sun kama mijin ‘yar ɗan majalisa da aka kashe a Borno

0
286

Rundunar ’yan sandan jihar Borno ta kama mijin marigayiya Fatima Alhaji Bukar da wasu da ba a san ko su wane ne ba suka kashe ta a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

A ranar Talata ce wasu da ba a kai ga gano su ba ne suka kashe Fatima a gidanta da ke Dikechiri Bayan Gidan Dambe a Maiduguri.

Rahotanni sun ce waɗanda suka kashe matar sun ɗaure ta da igiya, inda suka rufe bakinta don gudun ka da ta yi musu ihu tare da daɓa mata wuƙa a sassa daban-daban na jikinta, wanda a ƙarshe ya yi sanadin mutuwarta.

Wata majiya a cikin iyalan ta ce an kama mijin matar mai suna Adam Alhaji Ibrahim ne a ranar talata da daddare, bayan Gwamna Babagana Umara Zulum ya umarci hukumomi da su mayar da gawarta zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri domin a faɗaɗa bincike.

KU KUMA KARANTA: An shaƙe wuyan ‘yar ɗan majalisar dokokin jihar Borno ta mutu har lahira

A baya dai kafin umarnin Gwamnan, iyalan ta sun sanya ranar Laraba da ƙarfe 2:00 na rana domin yi mata jana’iza a gidanta da ke Maiduguri.

Gwamnan ya bayar da umarnin a bincika tare da bankaɗo aika-aikar tare da gurfanar da su gaban ƙuliya.

Leave a Reply