An bankaɗo asusun banki 570 da tsohon gwamnan Benuwe ke amfani da su

0
265

Gwamnatin jihar Benuwe ta zargi tsohuwar gwamnatin da ta shuɗe ta tsohon gwamna Samuel Ortom na PDP da yin amfanu da asusu banki 600.

Gwamnatin Benuwe ƙarƙashin Gwamna Hyacinth Alia na APC ya caccaki Ortom da ɓoye bayanan asusun banki sama da 570, inda ya nuna 25 kacal sa’ilin miƙa mulki.

Kwamishinan kuɗi da tsare-tsaren kasafin kuɗi na jihar, Michael Oglegba, ne ya faɗi haka yayin da tawagar ƙungiyar ‘yan jarida (NUJ) ta kai masa ziyara a Ofis ɗinsa ranar Talata a Makurɗi.

Ya ce bisa wannan dalili ne mai girma Gwamna Alia ya ba da umarnin rufe dukkan asusun gwamnati bayan ya karɓi mulki.

Kwamishinan kuɗi ya ƙara da bayanin cewa gwamnatin Ortom ta nuna wa Gwamna Alia asusu 25 ne kacal lokacin da ya karɓi ragamar mulki a watan Mayu.

Amma a cewarsa, bayanai daga hukumar kula da mu’amalar bankuna ta tarayya ya nuna gwamnarin Benuwe na da asusu sama da 600.

KU KUMA KARANTA: NDLEA ta bankaɗo ɗakin da ake haɗa sinadaran ƙwayar meth, ta ƙwato fakitin haramtattun ƙwayoyi da dama

“Lokacin da muka zo, mun nemi a bamu bayanan asusun banki kuma an gabatar mana da asusu 25. Da muka duba tsarin kula da mu’amalolin banki ya nuna jihar Benuwe tana da asusu sama da 600.”

“Saboda haka ne gwamna ya ga ya kamata a rufe dukkan waɗannan asusu domin gano me ke faruwa.”

Oglegba ya jaddada cewa gwamnatin Alia ya gaji bashin Naira biliyan 359 wanda ya ƙunshi basukan da ake bin ƙananan hukumomin jihar, kamar yadda Vanguard ta tattaro.

Leave a Reply