Ma’aikatan wutar lantarki sun garƙame hedikwatar KEDCO ta jihar Kano

Ma’aikatan wutar lantarki a ranar Litinin sun rufe kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano (KEDCO), bisa zargin gaza cire musu kuɗaɗen fansho da suka yi a cikin watanni 72 da suka gabata.

Ma’aikatan da ke ƙarƙashin ƙungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta ƙasa (NUEE) sun sha alwashin ci gaba da rufe kamfanin har sai an tabbatar da biyan kuɗaɗen.

Malam Ado Ririwai, Shugaban ƙungiyar na Arewa maso Yamma, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na NAN cewa ma’aikatan ba za su bari a ci gaba da irin wannan ɗabi’ar ba.

Riruwai ya zargi KEDCO da cin zarafin shugabannin ƙungiyar da ke ƙoƙarin yin magana a madadin ma’aikatan.

“Wannan aiki na mulkin mallaka ne; haƙƙin ma’aikata ne su yi yaƙi da abin da yake nasu,” inji shi.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta ba da umarnin a datse wuta da ruwa a Gaza

Shugaban ƙungiyar ya kuma zargi kamfanin da ƙin bai wa ma’aikatan kiwon lafiya na asali “duk da haɗurran da ke tattare da ayyukansu”.

Ƙoƙarin samun martanin hukumar ya ci tura yayin da duk ma’aikata, ciki har da ma’aikatan gudanarwa, an tilasta musu ficewa daga harabar hedikwatar kamfanin.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *