Wata matar aure ta watsawa mijinta asid a fuska, a kan naira 15,000

0
214

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ribas sun cafke wata uwar ‘ya’ya biyu da ta watsa wa mijinta Acid a fuska a kan rabon Naira 15,000 da aka biya kowane iyali a unguwar Nchia da ke ƙaramar hukumar Eleme.

Mummunan lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Asabar, 14 ga watan Oktoba.

Rahotanni sun bayyana cewa, matar ta samu rashin jituwa da mijin ta wanda ta yi zargin ya ƙwace kason Naira 15,000 da aka baiwa iyalan da kamfanoni na ƙasa da ƙasa da ke yankin suka ba al’ummar .

Ta ce mijin ya ƙi biyan ta kasonta na ‘ya’ya biyu daga cikin kuɗin.

A fusace matar ta zuba wa mijin nata acid sannan ta ƙwace masa katin ATM ɗin sa ta yi yunƙurin tserewa.

KU KUMA KARANTA: Uwargida ta zuba wa maigida tafasasshen man gyaɗa yana cikin barci, ta kwaɗa masa guduma ta gudu

Sakamakon haka mijin ya yi kururuwa wanda ya ja hankalin ‘yan banga. Ganin ‘yan banga sun biyo ta, sai ta gudu ta koma gida ta boye a cikin silin.

Daga bisani ‘yan banga sun sauƙo da ita daga silin na gidan, suka miƙa ta ga ‘yan sandan garin Eleme dake ƙaramar hukumar Eleme don ci gaba da bincike, yayin da aka garzaya da mijin zuwa wani asibiti da ba a bayyana ba domin neman kulawar gaggawa.

Leave a Reply