No menu items!

Sample Page Title

Date:

An yankewa Goni Muhammad da Saidu Sariki Hamani hukuncin ɗaurin shekaru bakwai a gidan yari bisa samunsu da laifin bayar da zinare na jabu, inda suka yi iƙirarin mallakin matar tsohon shugaban ƙasa Misis Patience Jonathan ne ga waɗanda ya saya.

Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC ta kama su ne a ranar Alhamis, 28 ga Satumba, 2023.

An gurfanar da su a ranar 16 ga Mayu, 2022, a gaban mai shari’a Aisha Kumaliya ta babbar kotun jihar Borno, Maiduguri, bisa tuhume-tuhume biyu da suka haɗa da haɗa baki da kuma karɓar kuɗi ta hanyar ƙarya har Naira 26, 492,000 (Miliyan Ashirin da Shida, ɗari huɗu da Naira dubu casa’in da biyu kacal).

KU KUMA KARANTA: Kotu ta ɗaure hakimi shekara biyar, bisa laifin safarar wiwi da miyagun ƙwayoyi a Sakkwato

Mai shari’a Kumaliya, a hukuncin da ta yanke, ta same su da laifi, ta kuma yanke musu hukuncin ɗaurin shekara ɗaya zuwa bakwai a gidan yari kowannen su bisa laifin haɗa baki da kuma shekara bakwai bisa laifin aikata laifin ƙarya.

Za su fara zaman gidan yari ne daga ranar da aka fara gurfanar da su a gaban ƙuliya.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...