Kotu ta ɗaure hakimi shekara biyar, bisa laifin safarar wiwi da miyagun ƙwayoyi a Sakkwato

0
256

Babbar Kotun Tarayya da ke Sakkwato, ƙarƙashin Mai Shari’a Ahmad Mahmud, ta yanke wa wani Hakimi, Alhaji Umar Mohammed (Ɗan Bala) hukuncin ɗaurin shekara biyar da rabi a gidan yari bisa zarge-zarge huɗu da suka haɗa da mallaka da kuma sayar da tabar wiwi kilo 436.38 da kuma magungunan sa maye da hukumar NDLEA ta gurfanar da shi a Oktoban 2022.

An yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru biyu akan kowane tuhume-tuhume na 1 da 2 tare da zaɓin tarar Naira miliyan 1, da kuma wata takwas akan kowanne, yahin da na 3 da 4 ba tare da zaɓin tara ba.

Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi ne ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi.

Leave a Reply