No menu items!

Sample Page Title

Date:

Akwai yiwuwar a yi wa kyaftin ɗin Portugal, Cristiano kuma ɗan wasan gaban Al-Nassr Cristiano Ronaldo za a yi masa bulala 99 idan ya koma Iran.

Jaridar Alfijir Labarai ta rawaito ɗan wasan wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar ya gana da mai goyon bayansa, mai zane Fatima yayin da yake tafiya zuwa Iran domin buga gasar cin kofin nahiyar Asiya da ƙungiyar Persepolis a watan Satumba.

Ronaldo ya runguma tare da sumbatar yarinyar, lamarin da ake ganin babban cin zarafi ne ga dokar Iran a wajen aurenta.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta yankewa shugaban Kiripto hukuncin ɗaurin shekaru 11 a gidan yari

Sai dai har yanzu ba a tuhumi tsohon ɗan wasan na Manchester United da Real Madrid a hukumance ba.

A halin yanzu Ronaldo yana tare da tawagar ƙasar Portugal yayin da suke shirin ƙarawa da Slovakia da Bosnia & Herzegovina a wasannin neman cancantar shiga gasar EURO a ranakun Juma’a da Litinin.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...