Isra’ila ta jefa dubban al’ummar Gaza cikin matsanancin matsalar rashin ruwa

0
158

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya a Falasɗinu ta ce a yanzu ruwa ya zama “al’amari na rayuwa da mutuwa” ga mutanen yankin Zirin Gaza bayan da Isra’ila ta katse ruwan da suke samarwa.

Hukumar ba da agaji ta Majalisar Ɗinkin Duniya da ke kula da ‘yan gudun hijirar Falasɗinu a yankin Gabas ta Tsakiya (UNRWA) ta faɗa a ranar Asabar cewa sama da mutane miliyan biyu ne ke cikin haɗari sakamakon ƙarewar ruwa.

“Ya zama batun rayuwa da mutuwa.  Ya zama dole, ana buƙatar isar da man fetur a Gaza a yanzu domin samar da ruwa ga mutane miliyan biyu,” in ji Kwamishinan UNRWA Janar Philippe Lazzarini.

KU KUMA KARANTA: Rikicin Gaza: Netanyahu na neman tayar da yaƙin duniya na uku

Ba a ba da izinin shigar da kayan agaji zuwa Gaza tsawon mako guda ba, a cewar hukumar.

Ruwa mai tsafta ya ƙare a Zirin Gaza yayin da tashar ruwan cibiyoyin ruwan jama’a suka daina aiki.  A yanzu dai an tilastawa Falasɗinawa amfani da gurɓataccen ruwa daga rijiyoyi, lamarin da ke ƙara barazanar kamuwa da cututtuka.

Leave a Reply