Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya cire birnin tarayyar ƙasar Abuja daga tsarin Asusun Ajiya na Bai-ɗaya (TSA)
Tinubu ya ɗauki matakin ne da nufin bayar da dama wajen bunƙasa ci gaban birnin ƙarƙashin jagorancin ministan Abuja Nyesom Wike, domin ba shi ƙarin iko kan kuɗaɗen da birnin ke tarawa.
Ministan Abuja, Nyesom Wike ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a taron manema labarai da ya gudanar ranar Juma’a a Abuja.
Asusun Ajiya na Bai-ɗaya (TSA) tsari ne da gwamnatin tarayya ta ɓullo da shi a 2015, da nufin sanya duka kuɗaɗen shiga da gwamnati ke samu a cikinsa, domin tabbatar da gaskiya da bin diddigin kuɗaɗen gwamnati.