‘Yan sanda sun kama ‘yan ta’adda ɗauke da makamai a Abuja

0
328

Sabbin motocin da rundunar ‘yan sandan ta ƙirƙiro ‘Anti-One Chance Squad’ ne suka damƙe motocin domin daƙile duk wata barazana da ke faruwa a babban birnin tarayya Abuja.

Jaridar Alfijir Labarai ta rawaito rundunar ‘yan sanda a babban birnin tarayya Abuja ta ce ta kama wasu motoci 10 da ake zargin an yi amfani da su wajen gudanar da ayyukan ta’addanci a yankin.

Kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Haruna Garba, ne ya bayyana haka a wata ganawa da manema labarai a ranar Juma’a a Abuja.

Ya ce sabbin motocin da rundunar ‘yan sandan ta ƙirƙiro ‘Anti-One Chance Squad’ ne suka damƙe motocin domin daƙile duk wata barazana da ke faruwa a babban birnin tarayya Abuja.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda a Nasarawa sun kama wasu mata biyu da laifin ba wa ‘yan bindiga makamai

A cewarsa, akasarin motocin da aka kama suna ɗauke da baƙaƙen gilashi, (Tinted) kuma a yayin bincike an gano gatari, da wuƙaƙe, da ake ganin ana amfani da su wajen gudanar da ayyukansu na aikata laifuka daga cikin motocin.

Ya ce a halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike a kan mutanen uku da aka kama da motocin.

Malam Garba ya ce jami’an rundunar ‘yan sanda reshen Zuba, a ranar 8 ga watan Oktoba, sun kama wasu mutane uku da ake zargi da laifin fashi da makami da kuma garkuwa da mutane.

Ya ce an kama waɗanda ake zargin ne biyo bayan wani ƙiraye-ƙirayen da aka yi musu kan shakkun wasu mutane a kusa da kasuwar ‘ya’yan itace ta Zuba.

“Jami’an ‘yan sanda daga sashin Zuba sun yi gaggawar zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka kama wani da ake zargin, wanda da ganin jami’an ‘yan sandan, sai ya ranta a na kare.

An kai ruwa rana da shi, in da daga bisani jami’an ‘yan sanda suka kama shi.

“A yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa cewa shi ɗaya ne daga cikin wasu ‘yan ta’adda da ake musu laƙabi da ‘yan biyar, sannan ya jagoranci ‘yan sanda suka kama wasu ‘yan ƙungiyarsa guda biyu,” inji shi.

A cewar CP, ‘yan sandan sun ƙwato bindigogin AK-47 guda biyu, mujallu biyu da harsashi 35 daga gidan waɗanda ake zargin.

Leave a Reply